Asabar 7 Nuwamba 2026 - 23:25
Gyaran Al’umma Yana Farawa ne da Gyaran Kai da Riƙo da Kyawawan Ɗabi’u

Hauza/ Limamin Juma’ar birnin Skardu da ke yankin Baltistan na ƙasar Pakistan, Hujjatul Islam Sayyid Baƙir Husaini, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa tsoron Allah, gyaran ɗabi’un al’umma da riƙo da koyarwar addini. Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da malamai suke takawa wajen bayyana gaskiya da shiryar da al’umma.

A cewar sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza yayin hudubar Juma’a da ya gabatar a babban masallacin birnin Skardu, Sayyid Baƙir Husaini ya yi kira ga al’umma da su ƙarfafa tsoron Allah, su gyara halayensu, tare da bin ƙa’idojin addini.

A hudubarsa ta farko, ya yi amfani da aya ta 12 a cikin Suratul Hujurat, da kuma wata magana ta Imam Ali (AS) wadda ya ce:

«أُوصِیکُمْ عِبَادَ اللهِ وَنَفْسِی بِتَقْوَی اللهِ وَنَظْمِ أَمْرِکُمْ»

Ma’ana: “Ya ku bayin Allah! Ina yi muku da kaina wasiyya da tsoron Allah da kuma tsara al’amuranku.”

Ya jaddada muhimmancin tsoron Allah, tsara rayuwa da kuma yin nazari kan ayyukan kai.

Limamin Juma’ar ya bayyana cewa samun rabauta a duniya da lahira yana tattare da tsoron Allah, gyaran kai da kyautata ayyukan mutum. Ya ce maimakon mutum ya riƙa bibiyar kurakuran wasu, ya kamata ya fara duba nasa kurakuran tare da gyara su.

Ya ƙara da cewa koyarwar addini ya kamata ta bayyana a cikin halayen mutum da mu’amalarsa da sauran al’umma. Ya bayyana cewa gudanar da Sallar Juma’a da halartar majalisun addini ba za su samar da cikakkiyar fa’ida ba, sai idan koyarwar da ake samu a cikinsu ta yi tasiri mai kyau a ɗabi’u da zamantakewar mutane.

Dangane da wasu munanan ɗabi’u da suka yaɗu a cikin al’umma, ya ce ba za a iya kawar da yaudara, zamba, rashin gaskiya da neman riba ta haram ba tare da tsoron Allah ba.

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa soyayya, zumunci da fahimtar juna a tsakanin ’yan uwa. Ya bayyana cewa son duniya da kwaɗayin dukiya sun fara shafar kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin iyaye, ’ya’ya da sauran ’yan uwa.

Ya kuma yi kira da a guji haddasa rikici tsakanin ƙabilu, dangi da iyalai, tare da kiyaye ladabi, kyawawan ɗabi’u da mutunta juna a cikin tattaunawa da mu’amalar yau da kullum.

A wani ɓangare na hudubarsa, malamin ya yi magana kan matsayin malamai da masu gabatar da hudubobi a cikin al’ummar Musulmi. Ya bayyana cewa bisa fikihun Shi’a Ja’afariyya, malamai da masu huduba suna da ’yancin gudanar da ayyukansu na addini, kuma babu wata gwamnati ko hukuma da take da ikon tilasta musu gabatar da huduba bisa ra’ayinta ko muradunta.

Ya ƙara da cewa yin shawara da tattaunawa tsakanin malamai abu ne mai muhimmanci, amma tilasta musu wasu ra’ayoyi ko umarni da ba su cikin nauyin da Shari’a ta ɗora musu ba, ba abin karɓa ba ne a kan mimbari.

A cewarsa, hudubar Sallar Juma’a wata muhimmiyar dama ce ta bayyana hukunce-hukuncen Allah da koyarwar Manzon Allah (S). Saboda haka, wajibi ne limami ya gabatar da gaskiyar addini cikin ’yanci da sanin nauyin da ke kansa.

A ci gaba da hudubarsa, ya yi tsokaci kan sauye-sauyen siyasar duniya, inda ya soki manufofin Amurka da Isra’ila da matakan da suke ɗauka kan al’ummomin da ake zalunta.

Ya kuma tuna da shahadancin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i, da sauran shahidan Iran da na Falasɗinu, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye manufofi da sadaukarwar da suka yi.

A ƙarshen hudubar, Sayyid Baƙir Husaini ya gabatar da rahoton tallafin kuɗin da al'ummar Baltistan suka tara domin taimakawa Iran. Ya bayyana cewa an tara sama da miliyan 430 na kuɗin Rupee, waɗanda bayan gudanar da binciken lissafi da tabbatar da gaskiyar yadda aka tattara su, aka miƙa wa hukumomin da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa Ambasadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan ya miƙa godiyarsa da gaisuwarsa ga dukkan waɗanda suka bayar da tallafin, yana mai jinjinawa ruhin imani, ikhlasi da soyayyar da al'ummar Baltistan suka nuna.

Haka kuma, an bayyana cewa za a sanya wani allo na tunawa da sunan al'ummar Baltistan a asibitin da abin ya shafa, domin tunawa da wannan gudummawa da nuna haɗin kai da suka yi.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha